Harin bamabamai da ya auku a kasuwar taminus ya rutsa da mutane fiye da dari daya da kuma jikata wasu da dama. Dalili ke nan da shugabannin Kirista da na Musulmi suka jajantawa wadanda suka yi asarar 'yanuwa da dukiyoyi.
Rev Soja Bewerang shugaban CAN na jihar Filato yace a matsayin kiristoci ya kawo gaisuwar ta'aziya zuwa ga iyaye da suka yi rashi da wadanda suka rasa 'yanuwa da dukiyoyi. Haka ma ya yiwa mijamiu da masallatai da suke fama da jana'izar wadanda suka rasu ta'aziya. Yace abun ya zo masu da mamaki sabili da sun dauka sun manta da wani hargitsi a jihar amma sai gashi ba zato ba tsammani bamabami sun tarwatse. Yace tunanensu ya koma akan abun da ya faru a Chibok suna rokon Allah a sako yaran da aka sace sai kuma ga wannan. Ya kira wadanda suka yi aika-aikar masu mugunta masu cin zarafin mutane. Yace kungiyar CAN bata ji dadin abun da ya faru ba kuma da babbar murya sun yi tur da shi. Ya kira jama'a da su kwantar da hankalinsu kada su bari wani abu ya taso. Yace zubar da jini ya isa. A yi hakuri da juna.
Ita ma kungiyar Jama'atul Nasril Islam ko JNI reshen jihar Filato ta bakin sakatarenta na yada labarai Malam Sani Mudi ta yi tur da harin bambaman. Malam Sani Mudi yace abun da ya faru aiki ne na ta'adanci. Yace suna allawadai da shi da wadanda suka yi shi. Sun kuma jajantawa wadanda suka rasa rai ko 'yanuwa ko sun yi asarar dukiya. Yace babu inda musulunci ya yadda da ta'adanci. Yace a Musulunci kowa an bashi ransa aro ne sabili da haka mutum bashi da iko ya dauki ransa ko na wani. Ya roki a dinga kai hankali nesa a duk inda irin wannan abun ya faru. Yace aiki ne ba na Musulmi ba kuma ba na Kirista ba. Wadanda suka yi ba mutane ne da zasu ce suna ikirarin yin hakan da wani addini ba. Ya godewa jami'an tsaro yadda suka dauki matakan gaggawa domin hana yaduwar lamarin. Ya kira duk shugabannin su dinga jan kunnuwan matasa domin a guji tada hankalin mutane.
Ga rahoton Zainab Babaji.