Yana zaune ne a Bama. Yace duk rashin tsaro idan ba ya zama dole ba babu abun da zai kaishi Maiduguri.
Tsakanin Bama da Maiduguri hanyar bata da kyau. Shi mazaunin garin yace gaskiya hanyar bata da kyau. Amma duk rashin kyau din ya fara ne daga wani gari da ake kira Kauri. Daga Kauri zuwa Bama to kowa baya cikin hankalinsa domin 'yan bindiga na iya harbi ko ta wace kusurwa, wato sama ko kasa hagu ko dama. Ko ta kan bishiya harbi na iya fitowa. Wurin da bashi da kyau bai wuce kilomita goma sha biyu zuwa sha biyar ba. Ga hanya bata da kyau ga babu tsaro. Tsakanin Shatimari da Aulari da suke da tazarar kimanin kilomita biyu tsakaninsu to kowace rana sai an kashe mutane.
Ya roki Ubangiji Allah Ya taimakesu a gyara hanyar a kuma tabbatar da tsaro. Kana ya roki gwamnatoci na hukuma da jiha da na tarayya su taimaka. Yace suna cikin dokar ta baci amma an barsu kara zube babu ingantacen tsaro. Yace yau idan mota ta dauki hatsi ko kayan masarufi ba zata wuce hanyar ba sai a tsareta an kwashe kayan a kashe mutanen ciki kana a koneta. Yace kama daga Bama zuwa Gwozah har Adamawa babu tafiya domin rashin tsaro. Kai duk wata hanya da ta fita daga Bama zuwa koina ba'a bi. Duk hanyoyin da suka shigo Bama 'yan ta'ada sun mamayesu tare da kare hanyoyin da duwatsu da 'yan bindiga. Duk wadanda suka gani da abinci zasu kwace su ce yaya zaka kaiwa wadanda basa bin addinin Allah abinci.
Ga karin bayani.