Babban daraktan hukumar yiwa kasa hidima a Najeriya, NYSC, Brigediya Janar Johnson Olawumi, ya nuna damuwa kan tura masu yima kasa hidima yankunan da ke fama da ta’addanci.
Olawumi, wanda tsohon shugaba Jonathan ya nada a Disamban bara ya dauki matakin hana Mata daga cikin masu hidimar sanya dogon hijabi da tuni hakan ya jawo zanga zanga, da rashin amincewa daga shugabanin Islama,
Ya zama wajibi mu kare masu yin hidimar nan dan haka abun takaici ne ‘yan ta’adda na amfani da Mata masu dogon Hijabi wajen kai harin kunar bakin wake, ba dai mu dauki wannan matakin dan kuntatawa wani addini ko wata alada bace da duk muke girmamawa.
Malami addinin Islama Sheikh Abdullahi Bala Lau, na ganin hukumar bata yi dogon nazari wajen daukar wannan matakin ba.
Ya ce idan har ana son zaman lafiya to dole abi umarni Allah ka bi umarnin Manzon Allah sai ya zaunar da kai lafiya. Wannan kasa tamu tana cikin lallura koina cewa muke a ci gaba da aduo’i, da rokon Allah ya kawo zaman lafiya, toh sharadin a roki Allah shine a tsare dokokin Allah.
Ba dalili bane don ana barna da Hijabi kuma ya zaman to zamu hana sanya Hijabi.
Brigediya Janar Olawumi, da sauran shuwagabanin sassan ma’aikatun Gwamnati na jiran ko a kyale su ko a sauke su daga mukamansu biyo bayan umarnin yi masu garambawul da shugaba Buhari ya bayar.