Gwamntin Masar tace harin da har wa yau ya jikata mutane 12 ya faru ne a wani otel mai suna Swiss Inn a garin El-Arish inda alkalan dake sa ido a zaben majalisar dokokin kasar ke zama.
Rundunar soji tace sojoji da 'yansandan dake sintiri a otel din sun bude wuta akan wata mota cike makil da bamabamai dake kokarin farma ginin otel, suka tarwatsata. Amma duk da haka sai da wasu mayakan biyu suka samu suka kutsa cikin otel din. Daya ya tada bam a dakin dafa abinci ko kicin dayan kuma ya nufi wani daki cikin otel din ya bude wuta.
Hukumomin Masar sun ce sun kashe mahara uku cikin lamarin yayainda ISIS tace mutanenta biyu ne kawai suka kai harin.
Reshen ISIS dake Masar ya dauki alhakin kai harin a wani jawabi da ya buga a yanar gizo. Da ma can kungiyar ce ta dauki alhaki kakkabo jirgin fasinjan Rasha a watan Oktoba 31 wanda ya kashe mutane 224.
Rasha ta amince harin 'yan ta'ada ya kakkabo jirginta daga bisani kuma ta karfafa kai hare-hare akan Raqqa babban birnin ISIS.