Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KOGI: PDP Ta Kira Ministan Shari'a da Shugaban INEC Su Yi Murabus


PDP
PDP

Matsayin da INEC ta dauka akan zaben jihar Kogi bai yiwa jam'iyyar PDP dadi ba har ma tace ministan shari'a da shugaban INEC kamata ya yi su yi murabus.

PDP ta ki ta amince da matakin da INEC tadauka na ba APC damar sake tsayar da wani dantakara ya maye gurbin marigayi Abubakar Audu da kuma damar ya gaji kuri'un marigayin.

INEC ta tsayar da biyar ga watan gobe a ranar da zata gudanar da zaben.

Nick Dazan mai magana da yawun INEC yace sun nemi shawarwarin masana shari'a kafin su dauki matsayin da suka dauka.. Yace idan PDP bata gamsu da matakin ba tana iya garzayawa kotu.

Yanzu dai ita jam'iyyar PDP tana barazanar kauracewa zaben.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG