Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Ba Karya Mu kai Musu Ba Ba Zasu So Muba


Mata a kasashen duniya
Mata a kasashen duniya

Kowane mahaluki nada dammar fadan albarkacin bakinsa a kowane lokaci yaso, amma abun la’akari da shi anan shine, wai kuwa mutane na fadi abun da kan zame musu alkhairi kuwa? Koma ace wanda kan iya zamowa hanyar datar da wasu? Baki daya dai abun dubawa a nan shine kasancewar wasu na ganin cewar maza sunfi mata karya a mu’amalar yau da kullun.

Wasu ‘yan mata da suka bayyana ra’ayoyinsu da cewar a zahirin gaskiya mata sunfi maza shirga karya a wannan zamani da ake ciki, don kuwa a lokutta da dama za’a ga mace tana yi ma maza karya don ta samu ta cinma wani burinta na daban, ko kuwa za’a ga cewar a tsakaninta da ‘yanuwanta mata ma ta kanyi musu karya, sukan yi aron kaya don su burge maza, ko tace ita ‘yar gidan wane ce alhali kuwa ba haka bane, dama da makamantan irin wadannan.

A bangare daya kuma wasu sun bayyanar da nasu ra’ayin da cewar maza sunfi shirga gaggarumar karya, suna ganin mafi akasarin maza makaryata ne a ko ina suke, domin su burinsu shine su mamaye zuciyar mace don haka saisu dinga yimusu karya har sukuwa matan su aminta, a wasu lokuttama za’aga cewar namiji kanyi gasa da abokanshi wajen yima mace karya, ko da aro wasu abubuwan burgewa ko karya da wasu abubuwan rayuwa, duk don ya burge wannan budurwar tashi ko iayayenta har a kaiga bashi itan. A wasu lokutta kuwa shikesa yawaitan mutuwar aure a tsakanin miji da mata.

Amma abun la’akari dashi a nan shine koma dai wa yafi karya, ya kamata ace a irin marra da ake ciki, ko wanne yayi kokarin fadin gaskiya, don ta fadin gaskiya ne kawai al’uma zasu samu zaman lafiya da ci gaban kasa baki daya. A lokutta da dama abubuwan da ke haddasa fituntunu a duniya baki daya ba wani abu bane, illa rashin fadin gaskiya wadda ita ke jagoranci komai a rayuwa 'dan Adam. Don haka mutane suji tsoron Allah a kowane hali suke su fadi gaskiya kokuma suyi shuru don wannan shine koyarwar kowane irin addini a duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG