Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutunmutumi Kan Zama Abokin Rayuwa Musamman Ga Yara


A kasashe da aka cigaba, muhimancin ilimi ya wuce ace dalibi ya rasa zuwa makaranta, ko dai don wata nakasa da Allah ya daura masa. A wata makarantar Firamari ta ‘Point Pleasant’ dake karamar hukumar ‘Glen Burnie’ ta jihar Maryland dake nan kasar Amurka.

Makarantar sun kirkiri wani mutun mutumi da kan dauki dalibi zuwa aji, don halartar darasi a kowane loaci, batare da dalibin na cikin aji da sauran abokan karatun shi ba. Amma dalibi zai samu damar bada tashi gudunmawa kamar yadda kowanne dalibi zai bada a cikin aji.

Cloe, yarinya ce mai shekaru 11 da haihuwa, tayi fama da rashin lafiya, da har tasa bazata iya zuwa makaranta ba, amma makarantar sun yi amfani da mutunmutumi da zai bata damar shiga aji don daukar darasi kamar kowa, amma tana daga gida.

Hakan ya bama dalibar damar samun ilimi batare da ta shiga aji ba, a sanadiyar rashin lafiyar ta. Kana tana samun damar bada nata gudunmawa a duk lokacin da hakan ya taso a cikin aji, kuma taje wajen wasa da cin abinci don tattaunawa da sauran abokanta, wanda hakan yana bata damar zama cikin walwala batare da damuwa da irin halin da takeci kiba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG