PDP tace ficewar da 'yan majalisar suka yi taka dokar kasa ne. Bayan sun fita daga jam'iyyar da suka tsaya zabe a karkashinta to sun yi asarar kujerunsu.
Barrister Tajudeen Shittu shi ne lauyan da ya shigar da karar a madadin jam'iyyar PDP. Yace suna gaban kotun ne domin ta fasara masu sashi na dari da tara na kundun tsarin mulkin kasar Najeriya dake cewa duk wanda ya canza sheka zuwa wata jam'iyya to ya rabu da kujerarsa ke nan. Yace idan kotu ta amince sun rabu da kujerunsu shi kenan. Suna kuma rokon kotu idan har ta amince da bukatarsu to ta sa hukumar zabe ta hanzarta shiraya zabukan cike gurabunsu.
Dan majalisa Abdul A. Abdulhamid dake wakiltar Minjibir yana cikin wakilai talatin da daya da zasu gurfana a gaban kotun. Yace kotu bata da hurumin da zata iya cewa su bar kujerunsu. Shugaban majalisar jihar shi ne tsarin mulkin kasa ya dorawa alhakin cewa su bar kujerunsu. Yace duk ranar da shugaban majalisa yace shi ba dan majalisa ba ne sai dai ya tafi kotu.
Shi kuwa Kabiru Alhasan Ririm shugaban masu rinjaye na majalisar cewa yayi suna ma mamakin jam'iyyar ta PDP saboda daukan wannan matakin domin akwai wasu da suka fita daga wata jam'iyya suka koma PDP amma ita idan danta ne yayi abu to ya yi daidai idan kuma wani ne yayi a sabanin ra'ayinta shi ne take gani ba'a yi daidai ba. Yace sabili da jam'iyya ta rabu gida biyu suna da ikon su zabi jam'iyyar da suke so kuma sun zabi APC inda suke daram dam.
Wakilin Muryar Amurka a Kano Mahmud Kwari ya nemi ya san ko wannan mataki da PDP ta dauka ka iya takawa masu canza sheka daga wannan jam'iyya zuwa waccan birki musamman bayan sun ci zabe.
Malam Abbati Bako daraktan cibiyar nazarin al'amuran siyasa da dimokradiya ta kasa da kasa mai ofishi a Kano yace za'a iya samun mafita amma sai shari'ar ta kai kotun koli inda zata zo karshe. Idan aka samu hukunci na cewa yin hakan daidai ne ko ba daidai ba to daga wannan lokacin ne za'a samu daratsi.
Yace irin wannan ya faru a shekara ta dubu biyu da bakwai lokacin Obasanjo. Ita kotun koli tace Obasanjo bashi da ikon cewa Atiku Abubakar ba mataimakinsa ba ne. A nan maganar aka kasheta kuma bata sake tashi ba. Wannan ma ta 'yan majalisa a nan kotun koli zata mutu.
Ga rahoton Mahmud Kwari.