Dan Majalisar, ya bada hujjar cewa jami'an tsaron dake wannan yanki sun fuskanci majalisar da hujjoji, wadanda su 'yan majalisar baza su iya tabbatarwa ba nan take, amma dalilan da yace sun bayar, babu yadda za'a yi 'yan majalisar su ki amincewa da sabonta dokar.
Wannan yunkuri wanda yake samun adawar jama'ar wadannan jihohi, suna masu cewa babu amfanin dokar, saboda kashe-kashe da kone-kone karuwa ma yake yi, balle ma sace dalibai masu yawa da aka yi a baya-bayannan, wannan ya nuna rashin amfanin dokar.
Yanzu dai jihohi Borno, Yobe da Adamawa, sun kwashe shekara 1 kennan, karkashin dokar ta baci, kuma a wannan watan kawai, an samu asarar rayuka sama da 1,500 a arewa maso gabas kawai, kuma akwai korafe-korafen dake cewa sojojin Najeriya basu da isassun kayan aiki, kuma suna tsoron tunkarar 'yan bindigan da ake cewa 'yan Boko Haram ne.