A cikin wata takardar sanarwa da mai baiwa gwamnan jihar Ibrahim Geidam shawara akan harkokin yada labarai, Abdullahi Bego, gwamnatin jihar ta umurci shugaban kasa da ya sauya salon yaki da ta'adanci domin dokar ta bacin bata haifar da wani da mai ido ba.
Abdullahi Bego yace takardar tamkar mayar da martani ne akan labarin da ya fito cewa shugaban kasa ya bukaci majalisa ta yadda ya sabunta dokar ta baci da ya sakawa jihohin Adamawa, Borno da Yobe. An kafa dokar ta tsawon wata shida kana an sbuntata na wani tsawon wata shida. Saura 'yan kwanaki wa'adin dokar ya kare. Yace idan an duba dokar bata haifar da komi ba. A aka sarin gaskiya ma abubuwa sai tabarbarewa su keyi. Maimakon sake sabunta dokar kamata yayi shugaban kasa ya sake salon yaki da ta'adanci. Du da dokar ta bacin an cigaba da kashe-kashe da jefa mutane cikin mawuyacin hali. Sabili da haka a dauki wasu matakan inganta tsaro amma ba yin anfani da dokar ta baci ba kuma.
Shigowar kasashen waje domin su taimaka ba dalili ba ne na sake sabunta dokar. Idan da an yi abubuwan da suka kamata da kasashen waje basu shigo kasar ba. Najeriya nada kwararrun sojoji. An sansu a kasashe da dama. Sun yi aiki a Saliyau da Liberia da Kwango da Sudan kuma sun ci nasara. Da sun yi hakan a cikin gida idan da an basu kayan aikin da suke bukata. Gwamna Geidam da wasu gwamnoni sun bada shawarwari da ba'a yi anfani da su ba.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.