Yayin da jihohin Adamawa da Borno da Yobe ke jiran sakamakon bukatar da shugaban kasa ya mika masu inda yake neman kara wa'adin dokar ta baci a jihohin uku da wata shida, al'ummomin Yobe sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da matakin farko da majalisun suka dauka.
Mutane na ganin matakin alama ce dimokradiya ta fara kankama a kasar. Wani Malam Ismaila Muhammed yace 'yan majalisar tarayya sun nuna masu sun san aikinsu. Yanzu sun fara yiwa talakawa aiki. Yace su da suke cikin jihohin uku su ne suke jin radadin dokar kuma su ne yakamata a tuntuba kafin a aiwatar da komi. Yace a yi masu adalci a ji daga bakinsu kafin a yanke hukunci. Sun ji dadin matsayin majalisun domin a jihohin uku kasuwanci ya lalace abubuwa sun baci sabili da haka su ba zasu amince da wata dokar ta baci ba.
Shi ma wani Sale Bakuro a garin Damaturu yace suna farin ciki da majalisun sabili da kin amincewa da bukatar shugaban kasa ba tare da yin bincike ba. Yace sun yi mamaki da jin cewa majalisun sun bayar da makudan kudi domin kare rayuka da lafiya da dukiyoyin jama'ar jihohin uku wadanda kuma basu samu ba.Sabili da haka kudurin 'yan majalisaun abun alfahari ne kuma kamata yayi a yaba masu. Yanzu suna ganin 'yan majalisun zasu share masu hawayensu ba tare da bata wani lokaci ba.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.