Babba Kaita yace ana sa dokar ta baci ne domin a shawo kan harakar tsaro to amma a Najeriya inda aka kafa dokar harkar tsaro sai tabarbarewa ta keyi. Kodayake irinsu basu yadda ba amma tun da dimokradiya a keyi an tabbatar za'a kara wa'adin dokar.
To saidai majalisar dattawa bata tsayar da shawara ba. Tace sai ta kara tuntubar masu ruwa da tsaki akan batun. Amma sanatoci daga arewa maso gabas sun bayyana ra'ayoyinsu. Sanata Ahmed Zanna daga jihar Borno, daya daga cikin jihohin da dokar ta shafa, yace hakkin shugaban kasa ne ya karesu amma cikin shekaru uku da suka gabata bai yi ba har ma ya kafa masu dokar ta baci ta shekara daya. Yanzu kuma yana neman ya sabuntata. Yace idan babu wani nufi kada ya sa masu domin basa so.
Shi ma Sanata Alkali Jajere daga jihar Yobe wadda ita ma tana cikin dokar ta baci ya dubi al'amarin ta kundun tsarin milki ne. Yace a duba kudun tsarin mulki sashe na 305. Dokar ta tanadi a yi wa'adin wata shida sau biyu. To an yi hakan. Dokar kuma bata bada izinin a yi na uku ba ko an ci nasara ko ba'a cigaba ba.
Shi kuma Sanata Bindoji Birila daga jihar Adamawa yana kira a sake sabon salo a magance ta'adancin da ya addabi kasar. Yace su basu ce a cire soja ba. Idan ma an ga dama a kara sojan amma a basu kayan aiki da suka dace a kula da su. Shi ma Sanata Ahmed Barata daga jihar Adamawa yace dokar ta baci ta hana mutane walwala.
Ga rahoton Medina Dauda.