Yace su dai basa goyon bayan a sake sabunta wa'adin dokar ta baci domin abubuwan da suka faru cikin watanni goma sha biyu a karkashin dokar basu da kyau. Yace sabunta dokar bashi da anfani idan aka yi la'akari da yadda Najeriya ke gudanar da abubuwa. Idan ba'a sake salo ba, ba za'a samu nasara ba. Ba doka za'a sake sabuntawa ba. Kamata yayi a ba mutane aikin yi yadda ba zasu shiga yin ta'adanci ba. Ba kowa damar samun aikin yi shi ne zai magance matsalar ta'addanci.
Game da bukatar majalisun Najeriya cewa suna son su samu bayani daga sifeton 'yan sanda da hafsan hafsoshin sojoji kafin su yanke shawara akan bukatar da shugaban kasa ya mika masu na neman sabunta dokar ta baci da wata shida sai Dr Baba Adam yace 'yan majalisun ba zasu yi wani abun kirki ba. 'Yan majalisar wakilai ka iya yin wani abu amma na dattawa ba zasu yi ko mi ba. Majalisar dattawa zata sake kara wa'adin dokar ta baci kamar yadda shugaban kasa ya ke bukatan a yi.
Dr Baba Adam yace cikin shekaru uku da suka wuce an kashe nera tiriliyon uku akan harkokin tsaron shiyar amma duk da haka sojoji basu da abunci balantana ingantattun kayan aiki. Duk kudin ana sacewa ne. Ya kamata majalisun tarayya su kula da jin dadin sojoji da kuma tanada masu ingantattun kayan aiki. Ko gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya shaida cewa 'yan ta'ada sun fi sojojin Najeriya makaman zamani.
Daga bisani Dr Baba Adam yace basa son a kara wa'adin dokar ta baci. Idan kuma har za'a yi to a sake salo. Kara wa'adin dokar har zuwa shekarar 2015 zai shafi zabe. Ma'ana ba za'a samu wata sabuwar gwamnati ba lamarin da ka iya haddasa wani tashin-tashina daban.
Ga karin bayani.