Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Jihar Adamawa Sun Kaddamar Da Yaki Da Fitsara


Wasu matasa kenan ke wasa albarkacin zaman lafiya
Wasu matasa kenan ke wasa albarkacin zaman lafiya

Kungiyoyin matasa a jihar Adamawa sun kaddamar da yaki da shaye shaye da banganci da sauran miyagun halaye

Majalisar Matasa a jihar Adamawa ta kaddamar da yaki da sha da kuma safarar muggan kwayoyi da banga da kuma tashe tashen hankula, a wani yinkuri na baya bayan nan na ceto yankin daga koma bayan zamantakewa.

Wakilinmu a jihar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito Sarkin Matasan Lunguda Mr Dulmiwilfan Tinde na bayyana cewa matsalolin da ke addabar matasan yankin sun hada da shaye-shayen kwayoyi da yawan sakin masu laifi da ‘yan sanda kan yi; sannan kuma ga babakeren da masu unguwanni ke yi kan abubuwan more rayuwa. Ya ce wata matsalar kuma ita ce ta halayyan alkalai.

Wakilin namu ya ce shi ma yankin Masarautar Bachama ya sha fama da fituntunun da su ka hada da na kabilanci da addini da dai sauransu. Ya kuma ruwaito shi ma Sarkin Matasan Bachama Mr Samaila More na cewa tuni su ka fahimci cewa idan babu zaman lafiya ba za a sami cigaba ba. Hatta addini ma ba za a iya yi da kyau ba muddun ba

zaman lafiya.
Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito Hukumar Yaki da Safara da Kuma Shan Kwayoyi (NDLEA a takaice) na nuna farincikinta da yadda matasan yankin, in ji ta, su ka yi matukar rage shaye shayen muggan kwayoyi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG