Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana dalilin da ya sa ya sallami Sakataren harkokin wajen kasar, Rex Tillerson, yana mai cewa ba su da ra’ayi iri daya kan batutuwa da dama.
Trump ya bayyana hakan ne ga manema labarai a yau Talata, inda ya ce “sun jima suna tattaunawa da Tillerson na tsawon lokaci, kuma suna jituwa sosai.”
Amma kuma irin tunaninsu ya banbanta, inji Trump.
Daga cikin batutuwan da Trumnp ya ba da misali a matsayin wadanda ba su da ra’ayi daya a kai, akwai batun yarjejeniyar nukiliyan Iran da aka kullaa a 2015.
“Idan ka kalli yarjejeniyar, sam ba ta da kyau, amma kuma shi yana ganin kamar ba ta da illa, ni ina so na rusa yarjejeniyar ko kuma na yi wani abu, shi kuma yana da ra’ayi daban, saboda haka, ba ma tunani iri daya.” Inji Trump.
Shugaba Trump ya kara da cewa, bai yi wata tattaunawa mai kwari da Tillerson kan shirin zama da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un ba.
“Ni kadai na yi gaban kaina, ba Tillerson ba ne, na yanke shawara ne tare da tuntubar jama’a da dama, amma ni kadai na yanke shawarata.”
Yanzu dai shugaban hukumar leken asiri ta CIA, Mike Pompeo ne zai maye gurbin Tillerson, yayin da Gina Haspel za ta maye gurbin Pompeo.
Trump da Tillerson sun jima suna samun sabanin, inda har akwai lokacin da rahotanni suka ruwaito cewa Tillerson ya kira Trump a matsayin “shashasha,” batun da shi Tillerson din bai musa ba.
Facebook Forum