Shugaba Donald Trump yace a shirye Amurka take ta dauki tsatsauran mataki dangane da kokarin Koriya ta Arewa na kera makamai masu linzami da za a iya dana musu kundojin nukiliya, amma kuma ya ce yana fata "matakin zai zamo wanda ya dace."
Kalaman shugaban sun biyo bayan sanarwar da Koriya ta Kudu ta fitar jiya Talata cewa, Koriya ta Arewa ta nuna cewa a shirye take ta fara tattaunawa da Amurka a kan dakatar da shirin makaman nukiliyarta.
Kalaman Trump na baya bayan nan a kan Koriya ta Arewa, sun sha bamban da irin barazanar da ya yi a baya, cewa Pyongyang zata huskanci wuta da fushi idan ta ci gaba da kera makaman kare dangi
Wani babban jami’in gwamnatin Amurka yace ra;ayin gwamnatin Trump a bude yake, amma kuma tana dari-dari da manufofi ko aniyar Pyongyang, yana mai cewa a cikin shekaru 27 da suka wuce, Koriya ta ARewa ta yi kaurin suna wajen "karya duk wani alkawari ko yarjejeniyar da ta kulla da Amurka da sauran kasashen duniya."
Jami’in, wanda ya nemi da a sakaya sunansa, ya kara da cewa, "yana da kyau kowa yayi la'akari da wannan, a kuma sanya ido a ga abinda zai faru."
Facebook Forum