Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Soji Sun Hallaka Buharin Yadi Da Wasu Mutane 35 A Kaduna

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Janar Christopher Musa (Facebook/Nigeria Defence Headquarters)
Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Janar Christopher Musa (Facebook/Nigeria Defence Headquarters)

Jami’an tsaro ne suka hallaka rikakken dan bindigar, wanda keda matukar hatsari tsakanin shugabanin ‘yan ta’addar arewacin Najeriya a shekarun baya-bayan nan, tare da wasu mutane 35.

Dakarun shiya ta 6, na aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Whirl Punch”, sun hallaka wani rikakken dan bindiga, Buhari Alhaji Halidu, wanda aka fi sani da “Buharin Yadi”, yayin wani samame a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Jami’an tsaro ne suka hallaka rikakken dan bindigar, wanda keda matukar hatsari tsakanin shugabanin ‘yan ta’addar arewacin Najeriya a shekarun baya-bayan nan, tare da wasu mutane 35.

A cewar sanarwar da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar an hallaka Buharin Yadi da sauran mambobin kungiyarsa ne a yayin wata musayar wuta tsakaninsu da dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Whirl Punch”.

“Kazamar musayar wuta ta rinchabe, yayin da aka yiwa ‘yan ta’addar ruwan wuta da makaman atilare a hayin almajiri. daga nan sai dakarun suka cigaba da fafatawa cikin jarumta, inda suka yiwa ‘yan ta’addar kwanton bauna, domin cimma burinsu. Kididdgar fari ta nuna cewar an hallaka akalla ‘yan bindiga 36 yayin arangamar.”

Daga bisani aka tantance cewar daya daga cikin wadanda aka hallaka din kachalla buharin yadi ne.

An hallaka ‘yan ta’addar ne tsakanin dajin idasu dake kan iyakar karamar hukumar giwa ta jihar kaduna da sabuwa ta jihar katsina.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG