Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Da Aka Kaiwa Wata Kasuwa A Kaduna Ya Hallaka Dimbin Jama’a


Yan bindiga
Yan bindiga

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun mamaye kasuwar ta “Maro Junction” ne da misalin karfe 4 da rabi na yammacin jiya Laraba, tare da bude wuta akan mutanen dake cikin kasuwar, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi.

Ana fargabar mutanen da ba’a san adadinsu ba sun hallaka bayan da ‘yan bindiga suka afkawa kasuwar “Maro Junction” dake gundumar Maro ta karamar hukumar Kajurun jihar Kaduna.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kisan, inda tace an jikkata mutane 5, sannan mutum guda ya rasa ransa a harin.

Saidai, mazauna yankin sun ce an harbe akalla mutane 12 har lahira yayin harin.

Da yake tabbatarwa da tashar talabijin ta Channels da afkuwar lamarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun mamaye kasuwar ta “Maro Junction” ne da misalin karfe 4 da rabi na yammacin jiya Laraba, tare da bude wuta akan mutanen dake cikin kasuwar, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi.

Ya kara da cewar mutane 5 sun jikkata, a yayin da mutum guda ya rasa ransa yayin harin, inda yace ana cigaba da bincike domin tantance ainihin adadin mutane da al’amarin ya rutsa dasu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ciagaba da cewar, bayan samun kiran gaggawa nan take sauran hukumomin tsaro suka garzaya zuwa wurin kuma yanzu haka suna bin sawun ‘yan bindigar domin kama su.

A cewar wasu mazauna yankin, ana zargin ‘yan bindigar sun kaddamar da harin ne daga dajin kanwa dake makwabtaka da kasuwar a karamar hukumar ta kajuru, inda daya daga sansanoninsu yake.

Kajuru na daga cikin kananan hukumomin dake yawan fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a jihar Kaduna.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG