Ana fargabar sabbin hare-haren ‘yan bindiga akan kauyuka da dama a kananan hukumomin Dutsinma da Safana na jihar Katsina sun hallaka mutane 30.
Dutsinma da Safana na daga cikin kananan hukumomin dake sahun gaba inda ake samun karuwar ayyukan ‘yan bindiga duk da matakan da gwamnati da hukumomin tsaro ke dauka na shawo kan matsalar masu tada kayar bayan a yankunan.
Shaidun gani da ido sun shaidawa tashar talabijin ta Channels a yau Juma’a cewar, an kaiwa kananan hukumomin da al’amarin ya shafa, da yawansu yakai 13, harin ne da yammacin ranar Talata 4 ga watan Yunin da muke ciki.
Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Dogon Ruwa, Sabon Garin Unguwar Banza, Tashar Kawai Mai Zurfi, Sarawar Kurecen Dutsi, Unguwar Bera, Durecin Kulawa, Larabar Tashar Mangoro, Sabaru, Ashata, Unguwar Ido, Kanbiri, Kunmawar Mai Awaki da Kunamawar ‘Yargandu.
Shaidun sun kuma bayyana cewar hare-haren sun firgita mazauna kauyukan wadanda sukayi hijira zuwa garuruwan dake da tsaro irinsu dutsinma.
Dandalin Mu Tattauna