Sojojin sun sami nasarar cafke wasu ‘yan ta’adda 5 lokacin da suka kai farmakin akan iyakar Mali da Nijer daga ranar 8 zuwa 18 ga watan nan na Yuni.
Sanarwar wadda ministan tsaron kasar Nijer Kalla Moutari ya sakawa hannu, na cewa wata rawar daji ta hadin gwiwar sojojin Nijer da takwarorinsu na Barkhane da gudunmowar asakarawan Amurka ta bada damar gudanar kakkabe ‘yan ta’adda a tsawon kwanaki 10 cif wato daga ranar 8 zuwa 18 ga watan yuni a arewacin Tongo Tongo iyakar Nijer da Mali.
Rawar dajin wadda aka yiwa lakabi da ACONIT ta bada damar samun nasarori inji sanarwar.
Ta ce dakarun Nijer da abokan hulda sun rattataka gaggan yan ta’adda kimanin 18 wadanda ke da’awa ma kungiyar IS reshen Sahara yayin da aka kama fursinonin yaki 5 cikinsu har da ‘yan Nijer 3, sannan sojojin hadin gwiwar sun cafke makaman yaki da dama ciki har da wadanda ‘yan ta’adda suka arce da su a yayin kwanton baunar da ya haddasa asarar rayukan dakarun Nijer a ranar 14 ga watan Mayun da ya gabata a kauyen Balle Beri dake kusa da Tongo Tongo.
A cewar wannan sanarwa ba a samu asarar rai ko 1 ba a bangaren sojojin gwamnati ballantana asarar kayan yaki, a yayin wannan rawar daji ta hadin gwiwa abin da ya sa ministan tsaro amadadin gwamnatin Nijer ya jinjinawa dakarun tsaro saboda wannan galaba da suka samu.
A yanzu haka ministan tsaron kasar Nijer ya kaddamar da zagaye a sassan yankin Tilabery domin karawa jami’an tsaro kwarin gwiwa a yakin da suke kwafsawa da ‘yan ta’addan da ke ketarowa daga arewacin Mali.
A wani abin da ke ci gaba da jefa ayar tambaya a zuciyoyin jama’a shine a cikin daren Talatar da ta gabata wayewar Laraba wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba sun hallaka ‘yan sanda 2 yayin da suka jiwa 2 munanann rauni a wata tashar binciken ababen hawa dake mashigar birnin Yamai.
Domin Karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum