A cikin jawabin da ya gabatar yace saboda dakatar da aika aikar 'yan Boko Haram gaba daya ya umurnin kara aikace aikacen dakarun a arewa maso gabashin kasar.
Janar Tukur Burutai ya cigaba da bada bayanin irin matakan da suka dauka.Yace sun kakkabe duk hanyoyin shiga da fita dajin Sambisa domin a takura kai-komon 'yan Boko Haram.
Saboda haka an mayarda hedkwatar shirin yaki ta rundunar ta uku na sojojin Najeriya zuwa Damaturu. Haka ma an mayarda birigedi na 27 zuwa Buni Yadi. Kazalika za'a tattara kayan aikin soji a Damaturu da zummar karfafa fafatawa da 'yan Boko Haram mai lakanin "Operation Lafiya Dole"
Babban hafsan yace an samarda motoci 106 cikinsu an sanyawa 45 manyan bindigogin kakkabo jiragen sama. Duka motocin aka aika dasu arewa maso gabas.
Janar Burutai ya kara da yiwa sojoji kashedi dangane da kibar jikinsu. Yace duk sojan da ya san kibarsa ta wuce kima to ya rageta nan da 15 ga watan Disambar wannan shekara.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.