Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kashe Akalla Mutane 21 A Jahar Barno.


Ma'aikatan kungiyar Red Cross suke dauke wata gawa, bayan harin da Boko Haram ta kai a Maiduguri
Ma'aikatan kungiyar Red Cross suke dauke wata gawa, bayan harin da Boko Haram ta kai a Maiduguri

Daga jahar Barno dake arewa maso gabashin Najeriya, mun sami rahotannin da suke nuni da cewa duk da irin nasarar da sojojin kasar suke bayani suna samu kan 'yan binidga, har yanzu 'yan kungiyar suna kai hare hare da haddasa hasarar rayuka.
Ko a cikin 'yan kwanakin akwai bayanai cewa 'yan binidgar sun kai hari a wasu sassan karamar hukumar Kukawa,suka kashe akalla mutane 21.

kamar yadda mataimakin shugaban karamar hukumar Habib Kekeno, ya tabbatar a hira da yayi da wakilin Sashen Hausa a yankin Haruna Dauda Biu.

Mallam Habib yace babu shakka jami'an tsao sun sami galaba kan 'yan binidgar ta yadda yanzu basu da makamai na zamani da suke kai hari dasu, sai dai wukake, ta hawa dawaki, ko ko babura.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG