Akwai alamun cewa za a cire wasu kasashen daga cikin shirin karin kudin fito da shugaba Donald Trump na Amurka ke dab da sanarwa a kan wasu karafa da ake shigowa da su Amurka daga waje.
Sakatariyar watsa labarai ta fadar White House Sarah Huckabee Sanders ta shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa, “muna sa ran shugaban kasa zai sa hannu a kan wani abu karshen mako, kuma mai yiwuwa ba zai shafi kasashen Mexico da Canada ba bisa dalilan tsaron kasa, kuma akwai yiwuwar cewa za a tsame wadansu kasashen ma a bisa irin wannan dalili."
Majiyoyi a fadar White House sun kuma ce mai yiwuwa a fito da wannan sabon shirin karin kudin fito na shugaba Trump da ake cacar baki sosai a kai a lokacin wani bukin sanya hannu da karfe 3:30 na rana, watau 9:30 na dare agogon Najeriya yau alhamis a fadar White House.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaci ta bakin wani babban jami’in Amurka yana cewa, za a fara aiwatar da matakin kimanin makonni biyu bayan shugaba Trump ya sa hannu a kai.
Facebook Forum