Congo ita ce babbar cibiyar barkewar cutar mpox da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana shi a matsayin yanki da ke bukatar gaggawar tallafi ta fuskar kiwon lafiya a duniya a watan da ya gabata.
Ana shirin kai alluran rigakafin cutar a cikin 'yan kwanaki don yaki da sabon nau'in cutar, yayin da shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi ya ba da izinin fitar da dala miliyan 10 na farko don yakar cutar.
Amma a harabar asibitin da ke garin Kavumu, inda aka dauki majinyata 900 da suka kamu da cutar a cikin watanni uku da suka gabata, ma’aikatan kiwon lafiya na matukar neman tallafi.
Babban likita Musole Mulamba Muva ya ce "magungunan suna ƙarewa ne a kowace rana."
“Akwai kalubale da dama da muke kokawa domin shawo kan matsalolinmu na cikin gida,” in ji shi, yana mai nuni da cewa tallafin da kungiyoyin kasa da kasa ke bayarwa ya na karewa ne cikin sauri.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna