‘Yan wasan gaba Julian Alvarez da Lautaro Martinez ne suka zura kwallaye bayan an dawo daga hutun rabin lokaci wanda ya tabbatar da nasara a wasan.
Canada suma sun samu dammawa sosai, inda suka samu wasu ‘yan damarmaki kadan a zagayen farko na wasan, ko da yake Argentina ta kusa zura kwallo ta hannun dan wasa Angel di Maria amma ya barar da damar da ya samu bayan da ya ruga da gudu da kwallo.
‘Yan wasan Lionel Scaloni sun samu nasarar cin kwallo a minti na hudu bayan an dawo hutun rabin lokaci, yayin da Lionel Messi ya bawa Alexis Mac Allister wani fasin da ya yi karo da mai tsaron ragar Canada Maxime Crepeau, sannan Alvarez ya zura kwallo a ragar Canada cikin sauki.
Canada ta yi kokarin farke kwallon da aka zura mata, amma dan wasan baya na Argentina Nicolas Otamendi ya yi abun da ake bukata na daidaita bayansu, kafin daga bisani Martinez da ya shigo wasan, Messi ya bashi fasin a minti na 88, inda ya zura kwallon da ta ba su nasara.
Wasan an fafata sosai, inda Canada ta samu wasu ‘yan damarmaki amma dai ba ta iya zura ko daya daga cikin su ba.
Shi ma fitaccen dan wasan Argetina Lionel Messi ya samu wasu damarmaki na zura kwallaye amma dai bai yi nasara ba.
Dandalin Mu Tattauna