Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aikin Ma'aikatan Shari'a: An Gudanar Da Babban Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Abuja


Yajin Aikin Kungiyar Ma'aikatan Shari'a Ta Najeriya
Yajin Aikin Kungiyar Ma'aikatan Shari'a Ta Najeriya

An gudanar da wani taron tattaunawa tsakanin kungiyar gwamnonin Najeriya da shugabannin majalisun dokokin jihohi, da kuma shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari, dangane da yajin aikin ma’aikatan shari’a.

Ma’aikatan na shari’a sun shiga yajin aikin sai baba ta gani a duk fadin kasar ne a ranar 6 ga watan nan na Afrilu, inda suke neman a bai wa bangaren na shari’a ‘yancin cin gashin kan sa, musamman a jihohi.

Duk da yake an yi ta tattaunawa da jagororin kungiyar akan bukatar su janye yajin aikin, ma’aikatan na shari’a sun sha alwashin ba za su janye yajin aikin ba har sai an aiwatar da ‘yancin cin gashin bangaren na shari’a a matakin jihohi tukunna.

Marwan Adamu, Shugaban Kungiyar Ma'aikatan Shari'a Na Najeriya
Marwan Adamu, Shugaban Kungiyar Ma'aikatan Shari'a Na Najeriya

Ko a jiya Alhamis ma an shirya gudanar da wani zama tsakanin Ministan kwadago Chris Ngige da shugabancin kungiyar ta ma’aikatan shari’a, amma kuma aka dage zaman.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban dandalin gwamnonin Najeriya, ya ce sun gudanar da taron ne tare da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a ofishinsa, da kuma wakilcin shugabannin majalisun dokoki na jihohi, inda suka tattauna akan bukatun ma’aikatan na shari’a da ke yajin aiki.

Tambuwal ya fadawa manema labarai da ke fadar shugaban kasa jim kadan bayan taron cewa, gwamnonin jihohi sun tattauna da shugabannin majalisun dokoki da kuma alkalin-alkalai na jihohinsu daban-daban dangane da lamarin, kuma za su ci gaba da tattaunawa da shugabancin kungiyar ma’aikatan shari’a domin kai karshen yajin aikin.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Akan haka ya yi kira ga ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin da suke yi, domin a cewar sa, “ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi.”

Gwamna Tambuwal ya ce “a wannan taro mun yi kokarin karshe na ganin an soma aiwatar da cikakken ‘yancin cin gashin kai ga bangarorin majalisar dokoki da na shari’a, kuma bayan karbar rahoton kwamitin kwararru akan lamarin, mun yi matsayar cewa za mu kuma haduwa a ranar Litinin mai zuwa, domin karasa shirye-shiryen karshe na magance matsalar baki daya.”

Kwanaki 10 da kungiyar ta ma'aikatan shari'a ta shiga yajin yajin aiki, lamarin da ya gurgunta ayukan shari'a a duk fadin kasar.

Manazarta kuma na ci gaba da bayyana irin koma bayan kasar ke fuskanta sakamakon yajin aikin ma'aikatan da suke cikin jerin manyan bukatu na kasa ga jama'a, musamman wajen tabbatar da bin doka da oda.

XS
SM
MD
LG