Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CBN Ya Kara Kudin Ruwa Zuwa Kaso 26.75


Shugaban babban Bankin Najeriya Olayemi Cardoso
Shugaban babban Bankin Najeriya Olayemi Cardoso

A yayin da hauhawar farashi ke kara tsananta, babban bankin Najeriya wato CBN ya sake kara kudin ruwa da maki 50, daga kaso 26 da digo 25 zuwa kaso 26 da digo 75 cikin dari lamarin da wasu ‘yan kasa ke ganin cewa yana kara tsananta tsadar kayayyakin abinci.

Gwamnan bankin CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana karin kudin ruwan ne bayan taron kwamitin manufofin kudin bankin karo na 296 da aka gudanar a birnin Abuja. Bankin CBN na ganin nan da dan lokaci ‘yan kasa zasu ga fa’idar matakin da ya dauka.

A bisa wannan matakin da bankin CBN ya dauka, Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin wasu masu gasa masara a kan titunan Abuja inda wani ya ce an sami dan sauki a samun masara saboda damina wata kuma ta ce atile da take saya a kan dubu 20 kowanne buhu ya koma dubu 30.

Shugaban Babban Bankin Najeriya Olayemi Cardoso da mataimakinsa Bala
Shugaban Babban Bankin Najeriya Olayemi Cardoso da mataimakinsa Bala

Kwamitin manufofin kudin CBN din dai ya bada dalilan da ya sanya aka dauki matakin kara kudin ruwan da maki 50. A bayaninta, jagorar sashen manufofin kudin CBN, Dakta Ladi Raulatu Bala-Keffi MNI, ta ce an dauki matakin ne don kawo sauki ga hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar rage yawan kudadden dake yawo a cikin kasa.

A wani bangare kuma, Dakta Raulatu ta yi karin Haske a kan batun maido da kudadden da aka dade ba’a yi amfani da su a asusun ba a bankunan kasuwanci zuwa babban bankin kasar don kar batagari su sami damar wawushe su ko kuma bankunan kasuwancin su ci gaba da juya su suna samun riba ba tare da cin moriyar masu asusun ba.

Membobin Kwamitin Kudin CBN
Membobin Kwamitin Kudin CBN

Najeriya dai na fama da matsalolin matsin tattalin arziki mafi muni a baya-bayan nan wanda ya yi sanadiyar tsadar rayuwa, makamashi, da masana tattali arziki suke cewa baya rasa nasaba da manufofin gwamnati kama daga cire tallafin man fetur a watan Mayun shekarar 2023 da tsarin canjin kudi na bai daya da aka bijiro da shi watannin kadan bayan karbar rantsuwar kama aikin shugaba Bola Tinubu

Saurari cikakken rahoton:

CBN Ya Kara Kudin Ruwa Zuwa Kaso 26.75
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG