Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hauhawar Farashin Kayayyaki Ta Ragu A Watan Yuli - NBS


Wata kasuwa a Najeriya
Wata kasuwa a Najeriya

Hukumar kididdiga ta NBS a Najeriya ta ce a cikin watan Yulin shekarar 2024, hauhawar farashin kayayyaki ta sauka zuwa kashi 33.40%.

A watan Yunin shekarar 2024 hauhawar farashin ya tsaya a kashi 34.19%.

Hukumar ta NBS ta wallafa wannan sabuwar kididdiga ne a ranar Laraba a shafukanta na sada zumunta ciki har da shafin X.

Hakan na nufin hauhawar ta ragu da maki 0.8% idan aka kwatanta da makin hauhawar a watan Yunin shekarar 2024.

Makonni biyu da suka gabata, ‘yan Najeriya suka fita zanga-zangar tsadar rayuwa saboda yadda farashin kayayyaki ke fin karfin talaka.

Sai dai kamar yadda kwararru a fannin tattalin arziki ke fada, ba kasafai irin wannan ci gaba da hukumar ta NBS take fitarwa yake kai wa kai-tsaye ga al’umar kasar ba.

“Muna fatan hakan zai sa CBN ya rage kudin ruwa.” In ji Femi @adebiyioluwafem.

“Shin haka yake a unguwanni? DatUrhoboMan a shafin X.

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG