A cikin wata sanarwan hadin gwiwar da wadannan kungiyoyin uku suka fitar jiya Alhamis sun bukaci sassan biyu da su gana kodai a kasar Habasha ko kuma a kasar Uganda karkashin jagorancin shugaba Yuweri Museveni.
Yanzu haka daiana sa ran tun daga jiya Alhamis Kwamitin Tsaro na MDD ya samar da wani kudiri wanda zai kawo karshen wannan tashin tashina na kasar ta Burundi, tare da barazanar kakaba wa duk wani daga cikin bangarorin biyu takunkunmi idan ya kawo wa yunkurin da akeyi na samar da zaman lafiya cikas.
Kwamitin ya bayyana takaicin sa kan yadda rikici ke kara zafafa a kasar ta Burundi ba tare dawani yunkurin samar da fahimtar juna ba tsakanin sassan biyu masu fada da juna.
Masu aikin diplomasiyya na MDD sunce majilisar zata gaggauta aikewa da masu aikin sasantawa a kasar muddin ba a samu zaman lafiya ba cikin dan kankanin lokaci.
Sai dai mahukunta a kasar ta Burundi sunce kasar bata huskantar ko wane irin barazanarkamar yadda ake rurutawa kuma ba wani batun kisan jama’a masu yawa.