Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BURUNDI: Ana Cigaba da Kidayar Kuri'un Zaben da Aka Yi Jiya


A Jewish woman named Renee Rachel Black and a Muslim man named Sadiq Patel react next to floral tributes for the victims of the concert blast, at St. Ann's Square in Manchester, Britain.
A Jewish woman named Renee Rachel Black and a Muslim man named Sadiq Patel react next to floral tributes for the victims of the concert blast, at St. Ann's Square in Manchester, Britain.

Duk da kaurajewar da 'yan adawa suka yiwa zaben shugaban kasar Burundi a gudanar da zaben jiya Litinin yau kuma ana cigaba da kidayar kuri'u.

Ana can ana ci gaba da kidayar kuri’u a Burundi, bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Talata, wanda sanadiyarsa dubban mutane suka tsere daga muhallansu cinkin ‘yan watannin da suka gabata domin gujewa aukuwar mummunan rikici.

Rahotanni sun ce ba a samu bayyanar masu kada kuri’a da dama a rumfunar zaben ba, wanda ya kasance cike da rudana ya kuma fuskanci kauracewar bangaren ‘yan adawa.

A ranar Alhamis mai zuwa ake sa ran za a fara bayyana sakamakon zabe, duk da cewa zaben ya sha sukar rashin sahihanci.

Zaben dai ya gudana duk da kiray-kirayen da kasashen duniya suka yi na cewa a dage zaben bisa dalilan mummunar zanga zanga da kasar ta fuskanta a ‘yan watannin na.

Jami’an gwamnati sun ce akalla mutane uku ne suka mutu, ciki har da wasu ‘yan sanda biyu, a wani fadan bindiga da tashin bama-bamai da suka auku gabanin zaben.

XS
SM
MD
LG