Shaidun gani da ido suka ce maharan sun umarci mutane da suke zaune a waje su shiga cikin ginin sannan suka bude wuta, suka kashe mutane bakwai nan take. Wasu biyu kuma suka cika daga bisani, sakamakon raunuka da suka samu.
Shaidun sun gayawa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa cewa maharan suna sanye da kayan aiki na 'Yansanda.
Kasashen duniya suna kara bayyana damuwarsu ganin tarzoma tana kara tsanani a kasar dake yankin Afirka ta Tsakiya, bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza yayi tazarce domin mulki wa'adi na uku.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka John
Kirby, ya fada ranar Asabar cewa, "Washington ta damu matuka, domin jin jami'an gwamnati suna amfani da lafuzza da zasu iya tada hankali." Da kuma shirin matakan tsaro da gwamnatin take shirin aiwatarwa a karshen makon nan, wanda yana iya tunzura jama'a su tada mummunar tarzoma.
Gwamnatin kasar ta umarci jama'a su mika makamansu ko kuma suyi kuka da kansu.
Shugaban Amurka Barack Obama yace yana shirin janye sunan Burundi daga jerin kasashe da suke amfana da wata damar cinikayya da Amurka saboda matakan murkushe 'yan hamayya da gwamnati take dauka tun fara mulki wa'adi na uku karkashin shugaba Nkurunziza.