Zababben shugaban kasar Najeriya Janar Muhammadu Buhari, ya ce ba zai yi alkawarin cewa gwamnatin sa tana da tabbacin samo ‘yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace guda 219 a garin Chibok dake arewa maso gabashin Najeriya a shekarar da ta wuce ba.
A cikin wani bayani da ya yi jiya Talata, lokacin da aka cika shekara ‘daya da sace ‘yan matan Chibok, ya ce, “bamu sani ba ko za’a iya ceto ‘yan matan Chibok.”
Janar Buhari ya kalubalanci gwamnati mai ci a yanzu da rashin kokarin neman ‘yan matan, ya na mai cewa “gwamnatin sa ba za ta yi abin da wannan gwamnatin ta yi ba”. ya kuma kara da cewa, a ranar da ya karbi ofis idan Allah ya yadda, kungiyar “Boko Haram za ta san iyakacin karfin mu.”
Kungiyar kare rajin ‘dan Adam ta duniya, Amnesty Internationl, ta ce mayakan Boko Haram sun sace mata a kalla dubu biyu a Najeriya, tun farkon shekarar ta 2014, tana kuma tilastawa yawancin matan wajen keta musu hadi, da maida wasu mayakanta.