Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Da Najeriya Ta Sayo Sun Sauka A Kano


Wani jirgin yakin Najeriya tare da sojojin kasar.
Wani jirgin yakin Najeriya tare da sojojin kasar.

A shekarar da ta gabata aka tura sojojin kasar zuwa Amurka don samun horo kan yadda za su sarrafa jiragen.

Zangon farko na jiragen yaki da Najeriya ta sayo guda shida kirar A-29 Super Tucano daga Amurka sun isa jihar Kano.

Kafofin yada labarai da dama a kasar sun ruwaito Darektan yada labarai na rundunar sojin saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet yana tabbatar da hakan.

Jiragen sun iso ne kwana biyu bayan da wani jirgin yakin kasar ya fadi a lokacin da 'yan fashin daji suka harbo shi a yankin jihar Zamfara. Sai dai matukin jirgin ya tsira.

Tun a makon da ya gabata, rundunar sojin Najeriyar ta ce jiragen za su iso kasar.

A shekarar da ta gabata aka tura sojojin kasar zuwa Amurka don samun horo kan yadda za su sarrafa jiragen, wadanda za a saka su cikin jerin jiragen yakin Najeriya.

Ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ne ya karbi jiragen tare da babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahaya da babban hafsan sojin sama Air Marshal Oladayo Amoa.

Najeriya ta sayo jiragen ne a ci gaba da yaki da take yi da ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji da suka addabi wasu sassan kasar.

Kasar na fama da mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin, da ‘yan fashin daji a arewa maso yammaci sai masu ikirarin a ware a kudu maso gabashi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG