Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Na Duba Yiwuwar Rage Ministoci


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (dama) a tattaunawarsu da Aliyu Mustapha na VOA
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (dama) a tattaunawarsu da Aliyu Mustapha na VOA

Sashen Hausa na VOA ya yi wata hira ta musamman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa, da tsaro da taron G7 da sauransu da tafiye-tafiyen da ya yi tare da Aliyu Mustapha.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, ya ce har yanzu bai yanke shawarar adadin ministocin da gwamnatinsa za ta nada ba, har sai ya yi nazarin rahoton da ya sa a hada mai kan halin da kasa ke ciki.

Buhari ya yi wannan bayani ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Sashen Hausa na VOA, inda ya ce halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da faduwar farashin mai a kasuwar duniya ya sa Najeriya a wani hali mai wuya.

“Wannan rahoto yana da karfi da gaske, yana da nauyin da gaske, nauyinsa shi ne, ma’aikatu nawa mu ke da su, kamar wajen guda 42 ne, yanzu tun da Najeriya ta karye ba ta da kudi, mai (fetur) bai sayuwa kuma babu tsada, shin za mu iya rike ma’aikatu (ministries) 42?, ko kuwa mu rike su akan 36 kawai, wato yawan jahohin Najeriya.” Buhari ya ce.

Ya kara da cewa “ban yanke shawara ba sai na ga wannan rahoto, wannan rahoto shi zai gwada mana halin da mu ke ciki a kan tsaro da arzikin kasa da kuma kudin da gwamnati ta ke da shi a bankin tsakiya (Central Bank) da kuma sauran bankuna da kuma bashin da ake bin mu.”

Basussukan Da Ake Bin Najeriya

Har ila yau shugaba Muhammadu Buhari ya kore ikrarin da ake yi na cewa ana bin Najeriya bashin kudi biliyan 600.

“Yanzu kana nan zaune aka kawo wannan rahoto, saboda haka ban karanta shi ba tukuna, amma shi mataimaki na inda ya samo na shi bayanin to wannan kuma ta rage, amma kuma ni ga wadanda na ba aiki sun kuma yi aikin sun kawo mini, sai na yi nazirin wannan aiki tukuna sannan za a yi ministoci, sannan dan cajin da za a yi a yi, saboda za mu iya gayawa al’uma ga fa abin da muka iske” Inji Buhari.

A ‘yan kwanakin nan ne kafafan yada labaran Najeriya suka ruwaito mataimakin shugaba Buhari, Farfesa Yemi Osinbanjo ya na cewa ana bin Najeriya bashin kudi biliyan 600.

Basusskan Da Jahohi Suka Bari

A cikin hirar da Sashen Hausa na VOA ya yi da shugaba Buhari, har ila yau ya tabo batun basussukan da aka barwa gwamnatocin jahohi, lamarin da ya kwatanta a matsayin “lalacewa” ta sa aka ma kasa biyan ma’aikata.

Akwai jahohi kamar 22 da wadanda ba su biyan albashion al’uma, lalacewar Najeriya ke nan har ta kai ga cewa ma’aikata ma ba a iya biyansu albashi.” Buhari ya kara da cewa.

Ya kuma jaddada cewa wannan rahoto da aka kawo mai shi ne zai tantance irin tafiyar da kasar za ta yi da batutuwan da suka shafi basussukan da sauran al’amuran kasar.

Taron Manyan Kasashen Duniya Na G7

Game da batun tafiyar da ya yi zuwa kasar Jamus domin halartar taron kasashen da suka fi karfin masana’antu a duniya na G7, Buhari ya ce da yawa daga cikin kasashen sun nuna aniyarsu ta taimakawa Najeriya.

“Yawancinsu sun yadda za su taimakawa Najeriya, kuma sun nuna da gaske suke yi, to amma na sa a duba, babban wahalar ita ce rashin tsaro na arewa maso gabas, batun Boko Haram wadanda suka ce sun yadda da kungiyar ISIS, wannan babbar kungiya ta ‘yan tawaye wadda ake fada da ita a Iraqi da Syria da sauransu."

Taron Wasu Kasashe Da Ke Makwabtaka Da Tafkin Chadi

A ranar Alhamis ne aka gudanar da taron wasu daga cikin kasashen da ke kusa da Tafkin Chadi domin lalubo hanyoyin da za a maganace matsalar hare-haren Boko Haram, inda Najeriya ta jajirce sai an ba ta jagorancin runduna ta musamman da za a kafa.

A yayin hirarsa da wakilin VOA Aliyu Mustapha, shugaban ya yi karin haske kan dalilan da ya sa ya ke ganin Najeriya ce ta fi cancanta a bata ragamar jagorancin rundunar sojin inda ya ce nacin da Najeriya ta nuna ba zai kawo cikas ba.

“Cikas din mai zai kawo? Fadan ba a Najeriya a ke yin sa ba? har ta kai ga su Nijar da Chadi da Kamaru suna taya mu fada, to kuma a kai wani wuri, nan ne filin dagar, shi ya sa muka ce a yi shi a nan.” Inji Shugaba Buhari.

Ga cikakkiyar tattaunawar da Aliyu Mustapha ya yi da shugaba Muhammadu Buhari:

Buhari Na Duba Yiwuwar Rage Ministoci 5’39”
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG