Babban jami’in watsa labarai na Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya halarci taron ne bayan goron gayyata da aka mikawa Najeriya sabon shugaban naya je ya gabatar da bukatun kasarsa wanda ya ke so kasashen su taimaka mata ta fuskar masana’antu.
“Ka san su suka gayyace shi, daya ke nan, kuma ba wai gayyata kawai su ka mai ba, sun ce ne ya yi lissafin wacce irin gudunmuwa ya ke so kasashe masu arzikin masana’antu su yiwa Najeriya.” Inji Malam Shehu.
Ya kuma kara da cewa ganin wannan goron gayyata, Buhari tuni ya riga ya shirya bukatun da zai gabatarwa kasashen a taron.
“Saboda haka a yanzu haka, ya zo da lissafin abin da ya ke ganin zai zama alheri ga Najeriya da mulkinsa.” Malam Shehu ya ce.
Ya kuma kara da cewa, Buhari zai gtana a gefen taron da shugabannin da dama ciki har da shugaban Bankin Duniya.
A daya bangaren kuma, tuni taron ya fara gudana a yau Lahadi, inda hankali ya fi karkata kan rikicin kasar Ukraine da matsalar basussukan da ake bin kasar Girka.
Sannan wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da taron ba tare da shugaban Rasha Vladmir Putin ba tun bayan da Rashan ta karbe yankin Crimea, lamarin da ya mayar da taron zuwa kasashen G7 a maimakon G8.
Ga karin bayani a tattaunawar Bello Habeeb Galadanchi da Malam Garba Shehu: