Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Fa'idar Shugaba Buhari Ya Halarci Taron G7?


Shugaba Buhari a Taron G7
Shugaba Buhari a Taron G7

Yau litinin aka fara taron kolin kasashe masu arzikin masana'antu a Jamus, Shugaba Muhammadu Buhari yana cikin shugabannin da suke halartar taron.

Litinin din nan za'a fara taron koli na kasashe masu arzkin masan'antu a Jamus.

Shugaban Amukr da sauran shugabanni kasashe da suke cikin wannan kungiya tuni suka isa wajen taron.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana halartar wannan taro bisa gayyatar da shugabanni dake cikin wannan kungiya suka yi masa.

Sai dai tafiyarsa ba ko wani dan Najeriya ne yake goyon bayansa ba. Alhaji Abdulkadiri Balarabe Musa, yana cikin wadanda suke ganin bai kamata ace shugaban yana hulda da shugabannin kasashen da har yanzu suke neman su ci gaba da yiwa kasashe kamar Najeriya mulkin mallaka.

Alhaji Balarabe Musa, yace mafi da cewa yanzu shine shugaba Buhari ya maida hankali wajen hada kan Najeriya, da kuma gyara tattalin arziki. Sannan daga bisani ya fara hulda da irin wadannan kasashe.

Amma kakakin jam'iyyar APC Alhaji Lai Mohammed yace, halartar wannan taro yana da muhimmancin gaske, domin idan ma akwai wata manufa, zuwa taron ne zai bada damar a gane abunda suke kullawa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG