Shugaban mai shekaru 74 ya bar Nigeriya a ranar 19 ga watan Janairu domin zuwa asibiti a duba lafiyarsa da ba a bayyana ainihin abin dake damunsa ba.
Amma jami’an gwamnati sun bayyana cewa ba wani abu bane na a-zo-a-gani, ba tare da sun bayyana hakikanin menene ke damun shugaban ba.
A yau Laraba, Ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya ce shugaban kasar ba’a asibiti ya ke ba, inda ya ce “ina tabbatar muku da cewa shugaban kasa yana nan cikin koshin lafiya kuma baya cikin wani hadari,” kamar yadda ya fadawa manema labarai a Abuja.
Mukaddashi kuma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kara jaddada kalaman Minisitan inda ya fadawa manema labarai cewa ya yi magana da shugaban kasa "kuma ya na cikin koshin lafiya."
Amma duk da haka, jawabin bai gamsar da wasu 'yan Nigeriya ba.
Tun bayan da ya karbi mulki a shekarar 2015, wannan shi ne karo na biyu da shugaba Buhari ya ke tafiya kasar waje domin neman magani.