Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitocin Shugaba Buhari A London Sun Bukaci Ya Dakata Komawa Najeriya


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yau ya kamata shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kama aiki a ofishinsa a karshen hutun kwanaki goman da ya dauka to amma likitocin dake kula da lafiyarsa sun bukaci ya jinkirta komawa gida Najeriya sar sai sun gama wasu bincike.

Yanzu dai an dake komawar shugaban Najeriya saboda haka ne me ya rubutawa majalisar kasar ta kara masa kwanakin hutu.

Kakakin shugaban Malam Garba Shehu yace shugaban ya rubuta wasika zuwa majalisa inda ya bukaci a kara masa kwanaki bisa hutun da ya dauka sanadiyar bukatar likitocin dake duba lafiyarsa a London kasar Ingila.

Malam Garba Shehu ya shaidawa jama'ar kasar cewa babu wani abu na tashin hankali ko kuma wata damuwa ko kuma a ce lafiyar shugaban ta tabarbare. Yace duk wadannan basu ma taso ba.

Cikin takardar da shugaban ya rubutawa majalisa bai sa iyaka ba ko lokacin da zai dawo saboda tsayar da ranar dawowa yanzu baya gareshi. Ya danganta ne da sakamakon binciken likitocin.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG