Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Buhari Nada Masaniya Kan Amsar da Fadarsa Ta Ba Majalisa Akan Sakataren Gwamnatinsa


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shirin Dimokradiya a yau yana tambaya ko shugaba Muhammad Buhari yana da masaniya akan amsar da gwamnatinsa ta ba Majalisar Dattawa akan zargin da take yiwa David Lawal Babachir sakataren gwamnati da majalisar ta zargeshi da yin munamuna a wata kwangilar biliyoyin nera

Kwamitin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dattawan Najeriya ya zargi Sakataren Gwamnatin da yin watanda da kudin kwangilar yanke ciyawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Kwamitin dake karkashin shugabancin Sanata Shehu Sani yace ya bankado wata badakala ta biliyoyin Nera da ta samu hannun Sakataren Gwamnatin Buhari a ciki. Bayan Majalisar ta gudanar da bincike ta sanar da gwamnati ta dauki matakin ladabtar da sakataren. Amma maimakon hakan sai ga wasika daga Fadar Gwamnati zuwa Majalisar inda tayi watsi da sakamakon binciken akan wasu dalilai.

Ga cikakken bayani a shirin Dimokradiya na Sahabo Aliyu Imam.

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:26 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG