Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Neja Ta Cafke Mutane da Take Zargin Suna Aikata Barna A Jihar


Alhaji Ibrahim K. Idris babban sifeton 'yansandan Najeriya
Alhaji Ibrahim K. Idris babban sifeton 'yansandan Najeriya

Rundunar 'yansandan ta cafke mutane sama da dari biyu tare da muggan makamai da ake zargin suna da hannu wajen aikata ayyukan kaiwa jama'a hari tare da kisan mutane da wawure shanu a yankin arewacin jihar

A 'yan kwanakin baya dai 'yan bindigan sun afkawa garuruwa da dama a kananan hukumomin Rafi da Shiroro inda suka hallaka mutane da dama tare da yiwa mata fyade da sace dabbobi masu dimbin yawa.

A wani taron manema labarai a Minna babban birnin jihar Kwamishanan 'yansandan jihar Zubairu Muazu yace sun sami nasarar cafke mutanen ne a cikin watan da ya gabata kuma a yanzu haka suna gudanar da bincike a kanasu.

Kwamishanan yace mutanen da suka kama sun taso haikan sun hana jama'a zama a kauyukansu. Kullum shiga kauyuka su keyi su kashe na kashewa kana su kwashe shanu tare da diban kayan abinci kana su bar gari. To amma da karin kayan aiki da jami'ai da babban sifetonsu ya aiko masu sun shiga kauyuka kuma sun sami nasara.

Daga cikin mutanen da aka nuna wa manema labarai har da wasu matasa guda ukku da suka kware wajen yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa. Daya daga cikinsu mai suna Muhammadu Sani yace shi yana sace mutane a yankin Mariga. Kawo yanzu ya sace mutane biyu wadanda ya kaisu daji. Yace an shirya a bashi nera miliyon ukku domin ya sakesu amma bai amsa ba tukunna dubunsa ta cika.

Mustapha Nasiru Batsari nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG