Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Kafa Kwamitin Rage Farashin Kayan Abinci


Rotimi Amaechi ministan sufurin Najeriya daya daga cikin kwamitin rage farashin abinci
Rotimi Amaechi ministan sufurin Najeriya daya daga cikin kwamitin rage farashin abinci

Gwamnatin tarayyar Najeriya da Muhammadu Buhari ke jagoranta ta kafa wani kwamitin manyan ministoci domin ya samo mata hanyar rage farashin kayan abinci a duk fadin kasar.

Ko shakka babu hau-hawan farashin abinci da na kayan masarufi ya zama wa 'yan Najeriya alakakai.

Kwamitin da ya kunshi ministocin sufuri da noma da albarkatun kasa da kudi da dai sauransu an bashi mako daya ya ba gwamnatin tarayya rahoto.

Sai dai dan majalisa Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya ce kafa kwamitin ya zo daidai da abun da ake kira ihu bayan hari.

Ya ce a tsari irin na dimokradiya dole sai gwamnati ta yi wani tanadi domin a yi maganin abun dake faruwa inda ya ce kwamitin an kafashi a lokacin da za'a ce an makara.

Hon. Ado ya ce idan gwamnati ta na son ta shigo harkar rage kudin abinci dole ne a ce ta yi tanadi a cikin kasafin kudi domin lamari ne da zai bukaci kudin gwamnati bayan da kwamitin ya mika rahotonsa.

Sai dai ya ce a cikin kasafin kudin da gwamnati ta gabatar babu abun da ya yi kama da wannan rage kudin abinci.

Wani manomi Musa Labaran ya ce aikin kwamitin ba zai yi tasiri ba idan ba an kawowa manoma sauki akan kayan aikin noma ba babu yadda farashi zai ragu

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG