Wannan tashin Bom din yazo ne kwana daya, bayan wasu mahara da ake kyautata zaton ‘ya’yan kungiyar Boko Haram ne, suka kai hari a cikin garin Gombe dake makwabtaka da Jihar Yobe, sannan suka farwa barikin sojoji da ofisoshin ‘yan Sanda.
Kunar bakin waken Lahadinnan ya haifar da fargaba da jimami, a cikin zukatan jama’a, musamman ma dai dai wannan lokaci da ake fuskantar hare-hare a wannan yanki, ganin cewa tashar nada cinkoson jama’a.
Tuni hukumomin tsaro suka killace wurin, kuma suna cigaba da gudanar da bincike akan aukuwar wannan lamari. Sai dai wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa suna zaton wadansu ne sanye da kayan sarki suka dasa wannan bom.
A halin yanzu jama’ar Najeriya na jiran babban zabe dake tafe nan da makonni 6, wanda da ranar 14 ga watannan na Fabrairu za’a fara, amma aka jinkirta shi saboda dalilai na tsaro. Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda yake yakin neman komawa kan karagar mulki na shan suka wajen masu kalubalantar gwamnatinsa, musamman wajen tabbatar da tsaro a kasar dake yammacin Afirka.