A bayan da hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce ta tanadi yadda 'yan gudun hijira zasu iya kada kuri'unsu a zabe mai zuwa, jam'iyyun hamayya da dama sun bayyana jin dadin wannan matakin wanda suka ce ya kawar da wata damuwar cewa idan ba a yi zaben a wasu jihohi ba, ana iya fuskantar matsalar sahihancin sakamakonsa.
Shi dai shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya fada wajen wani taro kan yadda 'yan gudun hijirar zasu kada kuri'unsu cewa su na iya yi a saboda za a yi amfani da na'urorin da zasu tabbatar da cewa sai wanda hoton yatsana ke jikin katin jefa kuri'a ne kawai zai iya kada kuri'a da wannan katin.
Wakilin jam'iyyun hamayya a hukumar zabe, Inusa Tanko, ya fadawa VOA Hausa cewa da ma tunanin ba za a iya gudanar da zabe a jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba, shi ne ya fi tayar musu da hankali.
Yace a yanzu babban kalubalen da suke son hukumar ta takala shine kare rayukan jama'a masu jefa kuri'a ta yadda zasu iya zuwa su yi zabe ba tare da fargabar rashin rayuwarsu ba.
Sai dai mataimakin darektan hulda da jama'a na hukumar INEC, Nick dazan yace zullumi game da tashin hankali bai ma taso ba, yana mai cewa sun yi shiri sosai domin tabbatar da cewa za a yi zaben da zai kai mizani.
Ya roki jama'a da su kwantar da hankulansu.