‘Yan ta’addan sun daure manoman ne suka musu yankar rago a kauyen Koshobe, inji kungiyar mai yaki da ‘yan ta’addan.
Mun gano gawarwaki 43 dukkanin su an yanka su tare da wasu da suka samu munanan raunuka, inji shugaban kungiyar, Babakura Kolo, wanda ya agazawa wadanda suka kubuta.
Mutanen da harin ya rutsa dasu, ma’aikata ne daga jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya mai nisan akalla kilomita dubu, wadanda suka je arewa maso gabashin domin yin aiki, inji wani dan kungiyar Ibrahim Liman wanda shima ya bada irin wannan alkaluma.
Wasu mutane tsakwas da suka bata, ana tunanin ‘yan ta’addan ne suka yi garkuwa dasu.
An kai gawarwakin kauyen Zabarmari mai nisan kilomita biyu daga inda za a yi jana’izar su a yau Lahadi, inji wani mazaunin wurin Mala Bunu wanda shima yake cikin wadanda suka yi aikin ceto.
A watan da ya gabata, mayakan Boko Haram sun kuma yanka wasu manoma 22 dake aikin ban ruwa a goanar su dake kusa da Maiduguri a wasu hare hare guda biyu.
Boko Haram da kungiyar ISWAP abokiyar gabarta mai alaka da IS, suna kara auna manoma da makiyaya da masunta a hare haren su, suna zargin su da leke asiri suna bada bayanai ga sojoji da kungiyoyi masu yaki da ‘yan ta’adda.
An kashe akalla mutum dubu 36 a cikin yakin masu ikirarin yakin jihadi, yakin ya kuma raba kimanin mutum miliyan biyu da gidajen su tun cikin shekarar 2009.