Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram ta Kai Hari a Garin Mainok a Jihar Barno


Jama'an da suka kauracewa gidajensu biyo bayan harin 'yan Boko Haram, sun samu mafaka a wata Makaranta, a Maiduguri, 9 ga Satumba 2014.
Jama'an da suka kauracewa gidajensu biyo bayan harin 'yan Boko Haram, sun samu mafaka a wata Makaranta, a Maiduguri, 9 ga Satumba 2014.

A cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ta bayar yace maharan sun dira kan kasuwar inda suka kashe mutane masu yawa.

kamfanin dillancin labarai na Reuters ya buga rahoton cewa mayakan sakai na Boko Haram sun aki hari kan wata kasuwa dake garin Mainok cikin jihar Barno, suka kasha mutane masu yawa.

Majiyoyi daga bangaren tsaro sun gayawa Reuters cewa an kasha akalla fararen hula 23, sauran kuma mayakan sakan ne da sojoji wadanda suke gadin garin suka kasha.

Rahoton ya kuma ce maharan sun saci kudi da abinci daga mutane da suke cike suna cin kasuwar.

Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane cikin shekaru biyar da suka wuce.

A ranar laraba ta makon jiya wasu 'yan binidga sun bude wuta kan wani zauren karatu a kolejin horasda malamai a kano suka kashe akalla mutane 15 wasu masu yawa kuma suka jikkata.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG