Kokarin da sojojin Najeriya keyi na tarwatsa ‘yan ta’adan Boko Haram ya kaiga kubutar da daruruwan mata da yara da suka kwashe wata da watanni a hannun ‘yan ta’adan. To saidai cikin fafatawar wasu sun rasa rayukansu saboda taka nakiyar da ‘yan ta’adan suka binne. Wadanda suka tsallake rijiya da baya sun ce nakiyoyi sun fashe yayin da manyan motocin sojoji suka takasu.
Hukumar bada agajin gaggawa ko NEMA tace mata da yara wajen su 275 da aka kubutar makon jiya daga wasu sansanoni a arewa maso gabashin Najeriya an kaisu sansanin ‘yan gudun hijira inda likitoci suke duba lafiyarsu kana masana akan kwantar da hankulan jama’a suke taimakamasu domin su sami natsuwar hankali.
Mata da yawa sun bayyana abun da ya faru yayain da sojoji suka zo su kubutar dasu. Sun fada cewa wasu matan sun boye a daji inda sojoji basu gansu ba amma sun rasa rayukansu yayin da motar sulken sojojin ta kutsa cikin dajin.
Wasu matan sun fada cewa sabilida yawansu ba duka ba ne suka iya shiga motocin sojoji. Dole wasu suka dinga takawa lamarin da ya kaiga mutuwar mata uku sanadiyar taka nakiya.