Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin Najeriyar ba ta fitar da adadin mutanen da ta sake kubutarwa ba, koda ya ke wasu rahotanni na cewa yawan matan ya kai 160.
Wani abu da ke jan hankulan mutane a yanzu shi ne, babu wanda ya saka idonsa akan wadannan ‘yan mata, koda ma ‘yan jaridu ba su damar kaiwa garesu ba.
A farkon makon nan Kakakin rundunar sojin ta Najeriya, Major Janar Chris Olukolade, ya bayyana cewa sun kubutar da ‘yan mata 200 da wasu manyan mata 93, bayan da suka kai wani samame a dajin Sambisa da ya kasance tunga ta karshe ga mayakan.
Dakarun na Najeriya sun ce sun kawar da sansanoni uku a lokacin wannan samame.
“Wannan labari ne mai dadi, amma muna kokarin mu samu tabbacin hakan ta hanya biyu, ko hoto ko kuma muryarsu, musamman manema labara da ke nan a Maiduguri, su samu a tabbatar musu, su ga wadannan matan a yid an jawabai.: In ji wani mazaunin birnin Maiduguri.
Ya kuma kara da cewa, “saboda jama’a da yawa suna kuka cewa mafi yawan lokuta idan an samu wata galaba ko kuma an samu nasara a wani bangare musamman sojoji, sai a ga labarin ya canja kama.” Ya ce.
Wannan ba shi ne karon farko da runudnar sojin ta Najeriya ke amai ta na lashewa ba, ko a watannin baya ta fito ta yi magana game da batun ceto ‘yan matan a kuma yakin da su ke yi da Boko Haram ammam sai ta janye.
Dajin na Sambisa, shi ne wajen da ake ganin 'yan kungiyar ta Boko Haram ke rike da 'yan makarantar garin Chibok da kungiyar ta sace a bara, wadanda har yanzu ba a jin duriyarsu.