Alhaji Abubakar Gamanbi shugaban masu sana'ar kamun kifi na jihar Borno kuma mai kula da yankin arewa maso gabashin Najeriya ya zanta da Muryar Amurka.
Jamhuriyar Nijar tana rike da kifinsu masu dimbin yawa bisa zarginsu da cewa su 'yan Boko Haram ne. Shugaban yace ya ziyarci kasar saboda ya rokesu su sako masu kayansu su sayar. Yace mutanensu dake cikin jamhuriyar abun tunane ne yanzu.
Alhaji Abubakar yace suna fargaban rayuwar 'yanuwansu dake tafkin Chadi domin gwamnatin kasar ta basu mako daya su fice daga yankin tafkin saboda sojojin kasar na shirya kai farmakin cikin tafkin inda suke zargin 'yan Boko Haram sun fake. Inji Abubakar yawancin mutanesu basu da ababen hawa domin haka ficewa daga wurin cikin lokaci zai yi wuya. Idan har suka wuce adadin da gwamnatin Nijar ta basu zasu iya rasa rayukansu. Bogu da kari ita gwamnati bata yi masu tanadin motoci ba da zasu kaisu tudun natsira.
Haka ma ita gwamnatin Najeriya bata aika da motoci ba da zasu kwashe mutane zuwa tudun natsira. Mutanen nada yawa. Wai sun kai kimanin dubu sittin zuwa saba'in. Yawancin mutanen 'yan Najeriya ne da suka je gudun hijira yayinda 'yan Boko Haram suka kai masu farmaki.
Ga cikakken bayanin Haruna Dauda Biu.