Rundunar sojin Najeriya ta fadi cewa ta kubutar da wasu mutane 150 da mayakan Boko haram su ka kame.
Mai magana da yawun rundunar Kanal Sani Usman, ya fada wa Muryar Amurka cewa dakarun sun ceto kusan yara 100 da mata 50 ranar Laraba yayinda suke kutsawa cikin dajin Sambisa dake arewa maso gabashin kasar. Dajin Sambisa dai akwai sansanoni ‘yan kungiyar Boko Haram da yawa, kuma ana kyautata zaton nan ne ‘yan kungiyar ta kai dubban ‘yan kasar da ta sace cikin ‘yan shekarun nan.
Sojojin Najeriya sunce sun kubutar da ‘yan mata 200 da mata 93 daga dajin na Sambisa ranar Talatar da ta gabata. Ceto matan da aka yi ya bada kwarin gwiwa akan ceto ‘yan mata 219 da aka sace a garin Chibok cikin shekarar da ta gabata. Tun sanarwar farko da rundunar sojan ta bada ta nuna babu daya daga cikin daliban na Chibok cikin ‘yan matan da aka ceto.