Sojojin Najeriya sun ce a ranar Alhamis din data gabata sun ceto wasu mata da yara guda 234 da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su a arewa maso gabashin kasar.
Sanarwa tasu tace wannan jimillah kari ne akan wadanda suka fara cetowa a lokacin da aka kai samamen baya a yankin.
Sojojin sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kai farmaki a dajin tare da maida hankali wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a dajin, sannan suna tarwatsa dukkan sansanonin ‘yan ta’addar da ke dajin.
A farkon makon nan ne dai aka ce an ceto kwatankwacin yawan wadanda aka ceta a yanzu daga dajin. An sami rahoton cewa daruruwan mata da ‘yan mata sun samin tsira tun daga makon da ya gabata.
Jummai Ali Maiduguri ta Muryar Amurka ta yi hira sa Kanar Sani Usman Kuka Sheka, Kakakin runduna ta bakwai dake Maiduguri don jin yadda lamarin yake.